Manhajar TalkSay da yadda ake amfani da ita

Mecece manhajar TalkSay?

Manhajar TalkSay sabuwar manhajar sada zumunta ce da kan bai wa mai amfani da ita damar tattaunawa da ƴan uwa da abokan arziƙi cikin sauti daga ko ina a faɗin duniya ta wayar salula.

Da wannan manhaja zaka iya yin hira kai da abokinka ko budurwarka, ko kuma da mutane da dama sama da guda ɗaya.

Abubuwan da kake buƙata domin rajista da TalkSay

  1. Lambar waya
  2. Hoto (DP)
  3. Suna
  4. Username

Yadda ake rajista da TalkSay

  1. Da farko za ka shiga Play Store sai ka yi searcing “TalkSay” ka yi downloading kamar yadda kuke gani a ƙasa.

  1. Daga nan manhajar zata baka dama ka sanya lambar wayarka banda 0 na farko.
  2. Za ka amsa tambayoyi daga Google saboda tsaro.
  3. Daga nan za a aiko maka da lambobin sirri da zaka shigar.
  4. Sai ka sanya hoto wato DP
  5. Sannan ka saka sunanka
  6. Sai username a taƙaice.

 

Yadda zaka yi amfani da manhajar TalkSay

Bayan ka kammala rajista zaka ga zaurukan da ake magana a daidai wannan lokaci kamar yadda kuke gani a ƙasa.

Rabe-raben zaure ko ɗaki a TalkSay

  1. Public – Buɗadden zaure wanda kowa da kowa zai iya shiga ya saurara
  2. Private – Zauren sirri da mutum zai buɗe ya tattauna da iya waɗanda ya ke so.

Duk zauren da ka shiga zaka fara sauraron abin da ake tattaunawa a ciki.

 

Yadda zaka yi magana a Zauren TalkSay

  1. Idan ka shiga zauren zaka ga wajen “Request”
  2. Da zarar ka danna, wanda ya buɗe group ɗin wato ‘Admin’ zai baka dama domin ka yi magana.

 

Yadda zaka bude Group da kanka

  1. Ka shiga “Create a Room”
  2. Sai ka saka sunan zauren
  3. Ka zaɓi ‘Public’ ko ‘Private’
  4. Sai ka zaɓi yare ‘Hausa’.
  5. Sai ka danna “Create a Room”.
  6. Shi kenan ka buɗe group ɗinka.

 

Yadda ake gayyatar aboki zuwa zaurenka na TalkSay

  1. A cikin zauren da ka buɗe zaka ga alamar WhatsApp daga ƙasa sai ka danna.
  2. Zai baka link da zaka aika zuwa ga wanda kake son gayyata.
  3. Wanda ka gayyata yana danna link ɗin zai bayyana a cikin zaurenka.

 

Amfanin da manhajar TalkSay za ta yi muku:

  1. Hira tsakanin saurayi da budurwa
  2. Tattaunawa tsakanin abokanan aiki/kasuwanci (meeting)
  3. Ƴan jarida na iya amfani da ita domin ɗaukar hira da mutum ko da baya ɗakin yaɗa labarai wato Studio.
  4. Kafafen yaɗa labarai za su iya amfani da TalkSay domin karɓar rahotanni daga wakilansu.

 

Note: Idan ka buɗe zaure kuma babu kowa a ciki, to zauren zai rufe kansa nan take.