Wannan shi ne darasi na farko da muka fara game da Blog, muna sa ran yin bayani filla-filla game da Blog da abin da ya ƙunsa.
- Menene Blog?
Blog shi ne duk wata kafa ko dandalin intanet da za a iya amfani da shi wajen wallafa bayanai domin isarwa ga jama’a.
Duk wani shafi ko manhaja da mutum zai iya buɗe asusu/yayi rajista ya aika da saƙo mutane su gani, wannan shi ake kira da Blog.
- Yaushe Aka Fara Yin Blog A Duniya:
Tarihi ya nuna cewa a ƙarni na 9 aka fara harkar blogging a duniya inda mutane kan wallafa bayanan da ya shafi rayuwarsu a kai, saidai ana yinsa ne a salon kimiyyar wancan ƙarnin.
A shekarar 1999 aka ƙaddamar da shafin blogging mafi suna wato Blogger.com mallakar kamfanin google.
A shekarar 2003 kuma aka ƙaddamar da WordPress wanda shi ne shafin Blogging da ke kan gaba a yanzu a duniya.
Akwai tarin shafuka da dama da ake yi a baya-baya da da kuma yanzu da suke ƙara ya waita.
Na san mai karatu zai iya tunowa da shafuka irinsu Wapka.Mobi ko su Xtgem.com da su Mywapblog.com.
- Shin Blogging Yana Bukatar Kashe Kuɗi?
Akwai Blogging na kyauta akwai kuma wanda sai mutum ya kashe kuɗi, saidai wanda ya kashe kuɗi shine zai fi cin ribar da ke cikin blogging.
Sannan akwai abubuwan da wanda ya biya kudi zai iya yi amman wanda bai biya ba ba zai iya yi ba.
Sannan adireshin wanda bai biya ba zai zama a free domain, saɓani wanda ya biya kuɗi zai iya sayen .com ko .com.ng koma .ng ya ɗora a kai.
Amma a zahiri da Blog na kyauta da wanda aka kashe masa kuɗi ko wanne ana iya wallafa bayanai wato posting na hoto ko bidiyo a duk sanda ake so.
- Menene Banbancin Blog da Websites?
Babban banbancin da yake tsakanin Website da Blog shi ne, shi Blog ana sabinta bayanansa a koda yaushe, wato dai wanda ya shiga Blog yanzu idan ya dawo anjima yana sa ran zai samu sabbin bayanai.
Shi kuwa websites bai zama lallai ko yaushe ana sabinta bayanansa ba, misali wani kawai bayanan kamfani ne ko kuma ƙungiya da ayyukanta.
Saboda haka shafukan kafafen yaɗa labaran da ake sabinta labarai dukkansu Blog ne.
A taƙaice ba kowane website ne Blog ba, amma kowane Blog Website ne.
A wasu website ɗin kamar na makarantu zaku ga suna ware shafi na musamman domin blogging wanda zaku ga ana kira da “Blog” ko “Blog Post”.
Zamu tsaya a nan, idan Allah ya kaimu a darasi na gaba, zamu ɗora a kan “Waye Blogger?”.