Ma’anar Social Media:
Social Media wato kafar sada zumunta, shi ne shafi ko manhaja da za ta bai wa mutum damar tattaunawa da wani ta hanyar rubutaccen saƙo, hoto, ko hoto mai motsi (video) ko kuma ta murya.
Mutane da dama kan tattauna batutuwa tare da musayar ra’ayi a waɗannan shafuka.
Ire-iren Social Media:
Daga cikin wadannan shafuka akwai Facebook, Twitter, Instagram, WhatsApp, Snapchat, LinkedIn, Snap Chat, da sauransu.
Meye banbancin Social Media da sauran kafafen yaɗa labarai?
Akwai banbanci da dama tsakanin social media da kuma kafafen yaɗa labarai na Radio da Talabijin.
Misali yanzu idan muna da tashar Radio ko Talabijin a Kano, idan baka saurari shiri a wannan lokacin ba to shirin ya wuce ka, sai dai in tashoshin na amfani da kafafen sadarwa wajen isar da saƙonsu.
Su kuwa shafukan sadarwa ko baka gani a lokacin ba in ka hawo daga baya zaka gani.
Sannan idan iya gari ake suararon Radio to su Social Media sun haɗa al’umma daga dukkan yankuna, wannan ya sanya saƙo a nan yafi saurin tasiri fiye da na Radio.
Radio a kan tantance sahihancin labari kafin a saki, amman shi Social Media kana iya ganin tarin ƙanzon kurege, kasancewar kowa Editan kansa ne.
Me ya kamata ka rubuta a social media?
Ɗan uwa ya kamata ka yi nazari ƙwarai da gaske ka san me zaka rubuta ko me zaka saka a social media.
- Ka kaucewa rubutukan cin zarafin wasu, domin za su iya maka ka a kotu domin neman haƙƙi
- Ka kaucewa saka hotunan da suke nuna ɓatanci ga wasu.
- Ka kaucewa saka hotunan tayar da tarzoma ko na faɗan ƙabilanci ko kuma na rikicin
- Ka kaucewa saka hotunan hatsari ko rikici da za su ɗagawa al’umma hankali.
- Ka yi amfani da salon shaguɓe ko gugar zana a duk sanda kake son isar da saƙo mai kama da wancan, kada ka kuskura ka kama sunan wani.
- Ka tabbatar da labari kafin ka yaɗ
- Ka dinga amfani da Hash Tag a rubutukanka.
Yadda Ake Kwafar Rubutu:
Idan kana amfani da Browser kamar su opera fire fox uc browser yadda zaka yi kwafi shi ne zaka danne ɗan yatsan ka a farko ko ƙarshen rubutun da kake son kwafa.
A nan zai baka “select” ko “copy” sai ka shiga zaka ga ya fara highlighting ya sa kala sai ka janyo shi har zuwa inda kake so sai ka danna copy zai saka maka “copied” shike nan.
Idan kana amfani da application na Facebook kuma to idan zaka yi copy kawai ka danne kan posting din, zai yi maka copy ko ya baka alamar copy sai ka danna, sai dai shi baya baka damar ka kwafi iya inda kake so sai dai gaba ki ɗayan posting ɗin, in yaso sai ka je ka ciri inda kake so.
A WhatsApp kuma yadda ake yin copy shi ne idan ka danne kan rubutun da kake son yin copy za ka ga yasa kala a kan sa, sannan a sama ya baka wasu alamu kamar zaka yi forwarding to a cikin alamun zaka ga wani shape ƙirar “square” sai ka danna zai saka maka “message copied” shi kenan, sai dai shi baya baka damar ka kwafi iya wajen da kake so sai dai gaba ki daya.
Yadda ake ajiye rubutun da aka kwafo wato “Pasting”
Abin da zaka yi shi ne kawai kaje ko ma wane guri ne indai wurin rubutu ne misali wps ko inbox din ka, ko kuma timeline ɗinka da kake posting ko group ko page dinƙa, sai ka danne ɗan ya tsanka a wajen, zai baka “past” sai ka danna shi kenan rubutun zai kawo a wajen sai ka tura ko kayi posting din sa.