Ƴan uwa barka da yau, a kullum ana ƙara samun rahotannin yadda masu kutse ke ci gaba da dandatse asusun da dama daga masu amfani da dandalin sada zumunta na Facebook.
Saidai hakan na da alaƙa da sakacin da mafi yawa ke yi game da ɗaukar matakan kariya, a wannan rubutu na yau, zamu kawo wasu daga hanyoyin da mutum zai bi domin bai wa asusunsa kariya ta musamman daga ƴan dandatsa.
- Yana da kyau ka dinga canja “Password” ɗinka aƙalla bayan sati ɗaya zuwa sati biyu.
Sharuɗan sauya password
A guji sanya lambobi 123456 ko sunanka, ko kuma lambar wayarka, sunan budurwarka, ko unguwarku, a’a yana da kyau ka sanya harufa da kuma lambobi, kai har ma da symbols kamar @”-+*&.
Sannan kada ka yarda ka sanar da wani wannan password ɗin naka.
A kula kada kayi amfani da password guda ɗaya a dukkan abubuwanka misali Password a Email da kuma Facebook da sauran abin da kake buɗewa duk su zama iri ɗaya, yin hakan ganganci ne da zai buɗe ƙofa ga masu kutse.
- Sanya ƙarin Email a kan account ɗinka: A ƙalla ina bada shawarar kayi adding Email kamar guda uku (3) a kan account ɗinka, ka ga kana da cikakken iko akan asusun,ta yadda duk wani motsi ko wani yunƙuri da aka yi kai tsaye zaka samu bayani.
Ka rufe emails ɗin ta yadda ba wanda zai iya gani
A settings na Email ɗin ka mayar da shi babu wanda zai iya ganin su sai kai kaɗai wato “only me” a yaren Facebook.
- Sannan lambar wayarka ta zamo tana aiki kana samun saƙonni a cikinta, da yawa lambobin da muka buɗe Facebook mun rasa layukan, amman har yanzu mun gaza cire lambar daga kan FB ɗin.
Rashin sauya wannan lamba shi ma na taka rawa wajen mu rasa asusunmu na Facebook.
- Ka kunna “Login Approval” da “Two-Step Verification.
Yadda zaka sanya shi ne ka bi wannan hanyar ka je :Home -> Account Settings -> Security -> Login Notification sai ka mayar dashi “Enable”
Wannan zai baka damar jin duk wani motsi na account ɗinka, sannan idan zaka yi login, dole sai an turo maka da code ko kuma kayi approving ta wayarka, sannan a nan ɓangaren zaka iya samar da “code generator” ta yadda zaka samar da wani code wanda kai kaɗai ne ka sanshi, idan ka zo yin login bayan password to shi ma zaka saka shi.
Latsa wannan link domin karanta cikakken bayani kan Facebook Protection
- Sanar da Facebook amintattunka
Zaɓar wasu amintattu daga Friend ɗinka, kamar Grantor kenan da za su tsaya maka idan ka samu matsala, zaka iya sanyawa a cikin Settings ɗinka na Facebook.
- Ka dinga yin log out duk sanda zaka sauka.
- Ka guji yin saving bayanan account ɗinka a waya ko Computer ɗin da ba taka ba.
- Ka tantance Link ko Application kafin bashi damar amfani da Facebook ɗinka
Sau da dama idan kana amfani da manhajoji ko wasu shafukan intanet su kan baka zaɓi na ka yi amfani da Facebook domin yin rajista da su, shi ne zaka ga an rubuta maka “Continue with Facebook”, ka tabbatar da ingancin ko wane daga ciki kafin ka amince, domin gudun faɗawa tarkon ƴan dandatsa.
- Ka tantance ta inda zaka riƙa shiga Facebook
Facebook.com ko manhajojin Facebook, Messenger da Lite, Business Suits ko Facebook Creator su ne zaka iya shiga kai tsaye, ka kula da wani abu bayan waɗannan da za a aiko maka domin shiga Facebook.
Ƴan dandatsa na yin amfani da link misali www.kano.facebook.com wato yin subdomain kenan, a ƙirƙiri wani adireshi na bogi, domin satar bayanai, ya zama dole ka lura da links da ake aika maka, shin Facebook.com ne kai tsaye ko akasin haka?.
- Ka dinga updating din browser ko application ɗinka lokaci zuwa lokaci.
- Ka daina yawan tura Friend Request ko yawan yin Accept, ka kula sosai wajen karɓar wanda baka san shi ba, yana da kyau ka duba Profile ɗin mutum kafin ka karɓe shi.
- Ka daina yawan yin sharing na wani link da baka tantance shi ba.