Sakamakon yawaitar saƙonninku game da Pi Network a yau cibiyar Sharfadi Technology ta gayyato muku Malam Ɗanladi Haruna ƙwararre a fannin ciniki da hada-hadar kuɗin intanet, inda muka miƙa masa tambaya kan Pi Network da kuma fashewarsa a watan Disamba, ga kuma amsar da ya bayar.
Menene Pi Network?
Shi Pi Network wasu ɗaliban Jami’ar Stanford ne masu bincike akan fasahar Cryptocurrency da Blockchain suka samar da shi a ranar 14 ga March, 2019. Shi yasa suke kiransa Pi watau 3.142 (alamar lissafi da ake kiyasta fadi ko girman Circumference).
A wata ukun farko, an samu kimanin mutane dubu 100 sun shiga.
A halin yanzu kuwa akwai mutane kimanin miliyan 25 a fadin duniya da suke ta amfani da manhajar suna tara kudin na Pi.
Sai dai har yanzu babu wani takamaiman farashi ko aiki ko manufa da wannan kudin na intanet yake da shi.
Har yanzu ana kan gwaji ne da musayar fasaha.
A halin da ake ciki, akwai masu sa kai da suka dukufa suna samarwa Pi din makoma kamar yadda masu tsarin suka bukata.
Haka kuma har yanzu babu wanda zai ce ga yadda wannan shirin nasu yake sai dai ana ganin cewar nan gaba kamar shekaru 8 masu zuwa zai samar da wani abin dogaro.
An yi hasashen cewar da za a fito da shi kasuwa yanzu, ba zai wuce Naira 3 ba. Masu nazari na ganin duka duka farashinsa ba zai wuce dala daya ba nan da 2028.
Ni a Hasashe na
Babu wata tsayayyar magana kan Pi a watan Disamba kamar yadda ake yadawa.
Ko da kuwa za su yi wani abu da za a amfana, to ba zai wuce na mutum daya cikin dubu ba.
A halin yanzu sun dauki gwajin yadda aikin tantancewar su na KYC zai kasance.
A Nijeriya, mutum 100 kadai suka dauka duk da cewar akwai miliyoyin ‘yan Nijeriya da suke ta bibiyarsu da minig a kullum.
Abin da na fi karfafawa shi ne, sun fi karkata ne wajen samun kudi ta hanyar tallace tallace.
Duk da suna ƙaryata wa amma lallai abin da suke samu a wajen talla kadai abin dubawa ne.