Ma’anar Blog da abubuwan da ya kamata ku sani game da shi

Wannan shi ne darasi na farko da muka fara game da Blog, muna sa ran yin bayani filla-filla game da Blog da abin da ya ƙunsa.

  1. Menene Blog?

Blog shi ne duk wata kafa ko dandalin intanet da za a iya amfani da shi wajen wallafa bayanai domin isarwa ga jama’a.

Duk wani shafi ko manhaja da mutum zai iya buɗe asusu/yayi rajista ya aika da saƙo mutane su gani, wannan shi ake kira da Blog.

  1. Yaushe Aka Fara Yin Blog A Duniya:

Tarihi ya nuna cewa a ƙarni na 9 aka fara harkar blogging a duniya inda mutane kan wallafa bayanan da ya shafi rayuwarsu a kai, saidai ana yinsa ne a salon kimiyyar wancan ƙarnin.

A shekarar 1999 aka ƙaddamar da shafin blogging mafi suna wato Blogger.com mallakar kamfanin google.

A shekarar 2003 kuma aka ƙaddamar da WordPress wanda shi ne shafin Blogging da ke kan gaba a yanzu a duniya.

Akwai tarin shafuka da dama da ake yi a baya-baya da da kuma yanzu da suke ƙara ya waita.

Na san mai karatu zai iya tunowa da shafuka irinsu Wapka.Mobi ko su Xtgem.com da su Mywapblog.com.

 

  1. Shin Blogging Yana Bukatar Kashe Kuɗi?

Akwai Blogging na kyauta akwai kuma wanda sai mutum ya kashe kuɗi, saidai wanda ya kashe kuɗi shine zai fi cin ribar da ke cikin blogging.

Sannan akwai abubuwan da wanda ya biya kudi zai iya yi amman wanda bai biya ba ba zai iya yi ba.

Sannan adireshin wanda bai biya ba zai zama a free domain, saɓani wanda ya biya kuɗi zai iya sayen .com ko .com.ng koma .ng ya ɗora a kai.

Amma a zahiri da Blog na kyauta da wanda aka kashe masa kuɗi ko wanne ana iya wallafa bayanai wato posting na hoto ko bidiyo a duk sanda ake so.

 

  1. Menene Banbancin Blog da Websites?

Babban banbancin da yake tsakanin Website da Blog shi ne, shi Blog ana sabinta bayanansa a koda yaushe, wato dai wanda ya shiga Blog yanzu idan ya dawo anjima yana sa ran zai samu sabbin bayanai.

Shi kuwa websites bai zama lallai ko yaushe ana sabinta bayanansa ba, misali wani kawai bayanan kamfani ne ko kuma ƙungiya da ayyukanta.

Saboda haka shafukan kafafen yaɗa labaran da ake sabinta labarai dukkansu Blog ne.

A taƙaice ba kowane website ne Blog ba, amma kowane Blog Website ne.

A wasu website ɗin kamar na makarantu zaku ga suna ware shafi na musamman domin blogging wanda zaku ga ana kira da “Blog” ko “Blog Post”.

 

Zamu tsaya a nan, idan Allah ya kaimu a darasi na gaba, zamu ɗora a kan “Waye Blogger?”.

Menene HashTag da yadda ake amfani da shi a Social Media?

Menene HashTag?

HashTag harufa ne ko kalmomi da ake amfani da su a kafafen sadarwa domin nuna alamar wani abu, ana fara shi da alamar # sannan abi bayansa da kalma ko harufan da ake son tagging, ba tare da tazara ba (space), hakan kuma shi yasa ake kiransa da HashTag.

Ana kuma amfani da shi wajen isar da saƙo ga mazauna gari ko wasu yankuna.

 

A ina ake amfani da HashTag?

Ana yin HashTag ne a cikin rubutu domin ƙara baza shi, wato ya ƙara yaɗuwa, ta yadda idan wani na neman wani abu da zarar yayi searching wannan hash tag din zai bada sakamakon rubutukan da aka yi da shi.

Wasu kafafen kamar blog, suna bada damar gurbin da zaka sanya kalmomin da kake son yin tagging, yayin da wasu kuma ake sakawa a gurbin rubutu wato wajen yin posting.

Gurbin da Blog suke bayarwa za su baka dama ka sanya kalmomin ko batun da kake ganin zai ɗauki hankali a kan wannan post ɗin a wajen HashTag.

A wasu daga waɗannan shafukan zaka iya yin following na hashtag ɗin ta yadda zaka dinga ganin duk wani rubutu da aka yi da wannan HashTag.

 

Yaya ake yin HashTag?

Yadda ake yinsa shi ne ana sanya # sannan sai a rubuta abin da ake so ya zamo tag din, misali #BasheerSharfadi shi ne HashTag ɗin da nake amfani da shi a kafafen sada zumunta, don haka idan mutum yayi searching wannan ko ya danna shi a cikin post ɗina, to zai kai shi ya ga duka sauran rubutukan da na yi, ko wani yayi amfani da wannan HashTag ɗin.

Idan wani ya kwafi rubutuna ko yayi sharing to indai da HashTag ɗin a ciki, ina shiga zan gansu gaba ki ɗaya.

 

Sharuɗan HashTag

  1. Ba a bada tazara wato Space, idan misali na rubuta #Basheer (space) Sharfadi to iya kalmar Basheer kawai na yi tagging shi yasa ake haɗe shi waje guda domin yin taggin ɗin abu mai ma’ana.

 

  1. Ba a saka alamar rubutu, sanya alamar rubutu a HashTag zai bada wahala idan wani yana son ya neme ka, ko kuma wani yayi rubutu game da kai yana so ya sanya, don haka bai kyautu ka saka alamomi irinsu _ ba.

 

  1. Sanya kalmomi ko harufan da ba za su wahalar da mutane wajen riƙewa ba, idan ka yi hakan zaka fi samun mutane da yawa, domin wani ko sauraro ya yi zai iya komawa yayi searching domin ganin wannan, hakama idan zai yi rubutu ba zai wahala ba wajen rubutawa.

 

  1. Tsayar da abu guda ɗaya wajen HashTag, kaucewa yin hashtag daban-daban misali yau mun yi #SharfadiBasheer gobe kuma mu yi #BasheerSharfadi a’a ka ɗauki guda ɗaya ka yi amfani da shi.

 

Salon HashTag

Ana yin amfani da salo wanda ba dole bane, wato fara harafin farko da babban baƙi, idan HashTag ɗin ya haɗa sama da kalma ɗaya shi ma haka misali, #WarAgainstFakeNews.

 

Ire-iren HashTag

  1. Akwai HashTag na kalmomi ko ƙungiyoyi da hukumomin Gwamnati ko kuma ɗaiɗaikun mutane.
  2. Akwai HashTag na gari kamar #Kano #Kaduna da sauransu, wanda idan ka yi kana fatana saƙon ya isa ga mazauna wannan gari, shi yasa zaku ga a posting musamman na Instagram da ƴan Kannywood ke yi suna bashi muhimmanci.

 

Misalan HashTag

#KNSG (Kano State Government), #FactCheking #FakeNews #CITAD#CDDWestAfrica #IDPs #Kano #FreedomRadioNigeria #BBCHausa #Hisbah.

 

Muhimmancin yin amfani da HashTag

  1. Isar da saƙon abin da ke ci muku tuwo a ƙwarya ga hukumomi, zaka iya tagging na hukumar da rubutunka ya shafa ta hanyar HashTag, an yi irin wannan lokacin da aka fara batun yaran Kano da aka sace aka sayar a Onitcha.
  2. Kamfanunuwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da masu sayen kaya na amfani da shi wajen bibiya, misali ina gangami yaƙi da shan ƙwaya, sai nake tagging ɗin kalmomin da suka shafi hakan, to zan ga masu irin wannan gangami a sassan duniya, su ma kuma za su ga nawa, ta nan zaku iya ƙulla alaƙa.
  3. Gayyato mutane zuwa wajenka, misalin irin wanda ake amfani a Arewa24 za a ce ku biyo mu a HashTag ɗin mu na #Zafafa10 da makamantansu, to ko a Rediyo kake shiri zaku iya ƙirƙira domin wannan.

 

Da wannan muke bada shawara ga kungiyoyi da marubutanmu kan su samar da HashTag da za su riƙa amfani da shi a rubutukansu.