Ma’anar Pi Network da raɗe-raɗin fashewarsa a Disamba

Sakamakon yawaitar saƙonninku game da Pi Network a yau cibiyar Sharfadi Technology ta gayyato muku Malam Ɗanladi Haruna ƙwararre a fannin ciniki da hada-hadar kuɗin intanet, inda muka miƙa masa tambaya kan Pi Network da kuma fashewarsa a watan Disamba, ga kuma amsar da ya bayar.

Menene Pi Network?

Shi Pi Network wasu ɗaliban Jami’ar Stanford ne masu bincike akan fasahar Cryptocurrency da Blockchain suka samar da shi a ranar 14 ga March, 2019. Shi yasa suke kiransa Pi watau 3.142 (alamar lissafi da ake kiyasta fadi ko girman Circumference).

A wata ukun farko, an samu kimanin mutane dubu 100 sun shiga.

A halin yanzu kuwa akwai mutane kimanin miliyan 25 a fadin duniya da suke ta amfani da manhajar suna tara kudin na Pi.

Sai dai har yanzu babu wani takamaiman farashi ko aiki ko manufa da wannan kudin na intanet yake da shi.

Har yanzu ana kan gwaji ne da musayar fasaha.

A halin da ake ciki, akwai masu sa kai da suka dukufa suna samarwa Pi din makoma kamar yadda masu tsarin suka bukata.

Haka kuma har yanzu babu wanda zai ce ga yadda wannan shirin nasu yake sai dai ana ganin cewar nan gaba kamar shekaru 8 masu zuwa zai samar da wani abin dogaro.

An yi hasashen cewar da za a fito da shi kasuwa yanzu, ba zai wuce Naira 3 ba. Masu nazari na ganin duka duka farashinsa ba zai wuce dala daya ba nan da 2028.

 

Ni a Hasashe na

Babu wata tsayayyar magana kan Pi a watan Disamba kamar yadda ake yadawa.

Ko da kuwa za su yi wani abu da za a amfana, to ba zai wuce na mutum daya cikin dubu ba.

A halin yanzu sun dauki gwajin yadda aikin tantancewar su na KYC zai kasance.

A Nijeriya, mutum 100 kadai suka dauka duk da cewar akwai miliyoyin ‘yan Nijeriya da suke ta bibiyarsu da minig a kullum.

Abin da na fi karfafawa shi ne, sun fi karkata ne wajen samun kudi ta hanyar tallace tallace.

Duk da suna ƙaryata wa amma lallai abin da suke samu a wajen talla kadai abin dubawa ne.

Toon Me: Yadda zaka canja hotonka zuwa Cartoon a waya

Kwanakin baya aka yi yayin jirkita hoto zuwa cartoon a kafafen sada zumunta, abin da ya ɗauki hankalin mutane da dama.

An riƙa musayar waɗannan hotuna tsakanin ƴan uwa da abokan arziƙi.

Masoya ma sun riƙa jirkita hotunan masoyansu domin dai nuna musu cewa ana tare, kuma akwai amana.

 

Yadda zaka mayar da hotonka zuwa Cartoon

Akwai manhajoji da dama da ke bada damar ka yi wannan a wayarka ta salula, amma zamu ɗauki guda ɗaya mu yi bayani a kansa.

  1. Ka shiga Play Store ka yi searching manhajar “Toon Me”.
  2. Ka yi downloading
  3. Ka buɗe manhajar
  4. Zai buɗo maka ire-iren zanen siffar mutane
  5. Sai ka zaɓi wanda kake so
  6. Daga nan zai baka dama ka ɗauko hoto daga cikin wayarka
  7. Sai ka ɗauko hotonka ko na wanda kake son yiwa na sa haka
  8. A nan zai baka inda zaka zaɓi girman hoton
  9. Sai ka dannan alamar kibiya a gefe
  10. Daga nan manhajar Toon Me zata fara aikin jirkita hotonka.
  11. Akwai alamar “T” domin ka yi rubutu a kan hoton, idan baka buƙatar rubutu sai ka wuce.
  12. Sai sauke hoto zuwa kan wayarka, zaka ga “Share & Save” sai ka shiga.

 

Yadda zaka cire logon Toon Me daga jikin hoton da ka gyara

Waɗannan manhajoji ana biyan kuɗi domin samun damar amfani da su, saboda haka idan baka biya ba, za su maƙala tambarinsu a jiki.

Yadda zaka cire tambarin ba tare da biyan ko sisi ba, shi ne ka danna kan tambarin zai baka zaɓi domin kallon tallan bidiyo a madadin ka biya kuɗi.

 

Ku latsa bidiyon da ke ƙasa domin kallon yadda zaku haɗa naku hoton:

Manhajar TalkSay da yadda ake amfani da ita

Mecece manhajar TalkSay?

Manhajar TalkSay sabuwar manhajar sada zumunta ce da kan bai wa mai amfani da ita damar tattaunawa da ƴan uwa da abokan arziƙi cikin sauti daga ko ina a faɗin duniya ta wayar salula.

Da wannan manhaja zaka iya yin hira kai da abokinka ko budurwarka, ko kuma da mutane da dama sama da guda ɗaya.

Abubuwan da kake buƙata domin rajista da TalkSay

  1. Lambar waya
  2. Hoto (DP)
  3. Suna
  4. Username

Yadda ake rajista da TalkSay

  1. Da farko za ka shiga Play Store sai ka yi searcing “TalkSay” ka yi downloading kamar yadda kuke gani a ƙasa.

  1. Daga nan manhajar zata baka dama ka sanya lambar wayarka banda 0 na farko.
  2. Za ka amsa tambayoyi daga Google saboda tsaro.
  3. Daga nan za a aiko maka da lambobin sirri da zaka shigar.
  4. Sai ka sanya hoto wato DP
  5. Sannan ka saka sunanka
  6. Sai username a taƙaice.

 

Yadda zaka yi amfani da manhajar TalkSay

Bayan ka kammala rajista zaka ga zaurukan da ake magana a daidai wannan lokaci kamar yadda kuke gani a ƙasa.

Rabe-raben zaure ko ɗaki a TalkSay

  1. Public – Buɗadden zaure wanda kowa da kowa zai iya shiga ya saurara
  2. Private – Zauren sirri da mutum zai buɗe ya tattauna da iya waɗanda ya ke so.

Duk zauren da ka shiga zaka fara sauraron abin da ake tattaunawa a ciki.

 

Yadda zaka yi magana a Zauren TalkSay

  1. Idan ka shiga zauren zaka ga wajen “Request”
  2. Da zarar ka danna, wanda ya buɗe group ɗin wato ‘Admin’ zai baka dama domin ka yi magana.

 

Yadda zaka bude Group da kanka

  1. Ka shiga “Create a Room”
  2. Sai ka saka sunan zauren
  3. Ka zaɓi ‘Public’ ko ‘Private’
  4. Sai ka zaɓi yare ‘Hausa’.
  5. Sai ka danna “Create a Room”.
  6. Shi kenan ka buɗe group ɗinka.

 

Yadda ake gayyatar aboki zuwa zaurenka na TalkSay

  1. A cikin zauren da ka buɗe zaka ga alamar WhatsApp daga ƙasa sai ka danna.
  2. Zai baka link da zaka aika zuwa ga wanda kake son gayyata.
  3. Wanda ka gayyata yana danna link ɗin zai bayyana a cikin zaurenka.

 

Amfanin da manhajar TalkSay za ta yi muku:

  1. Hira tsakanin saurayi da budurwa
  2. Tattaunawa tsakanin abokanan aiki/kasuwanci (meeting)
  3. Ƴan jarida na iya amfani da ita domin ɗaukar hira da mutum ko da baya ɗakin yaɗa labarai wato Studio.
  4. Kafafen yaɗa labarai za su iya amfani da TalkSay domin karɓar rahotanni daga wakilansu.

 

Note: Idan ka buɗe zaure kuma babu kowa a ciki, to zauren zai rufe kansa nan take.