Menene HashTag?
HashTag harufa ne ko kalmomi da ake amfani da su a kafafen sadarwa domin nuna alamar wani abu, ana fara shi da alamar # sannan abi bayansa da kalma ko harufan da ake son tagging, ba tare da tazara ba (space), hakan kuma shi yasa ake kiransa da HashTag.
Ana kuma amfani da shi wajen isar da saƙo ga mazauna gari ko wasu yankuna.
A ina ake amfani da HashTag?
Ana yin HashTag ne a cikin rubutu domin ƙara baza shi, wato ya ƙara yaɗuwa, ta yadda idan wani na neman wani abu da zarar yayi searching wannan hash tag din zai bada sakamakon rubutukan da aka yi da shi.
Wasu kafafen kamar blog, suna bada damar gurbin da zaka sanya kalmomin da kake son yin tagging, yayin da wasu kuma ake sakawa a gurbin rubutu wato wajen yin posting.
Gurbin da Blog suke bayarwa za su baka dama ka sanya kalmomin ko batun da kake ganin zai ɗauki hankali a kan wannan post ɗin a wajen HashTag.
A wasu daga waɗannan shafukan zaka iya yin following na hashtag ɗin ta yadda zaka dinga ganin duk wani rubutu da aka yi da wannan HashTag.
Yaya ake yin HashTag?
Yadda ake yinsa shi ne ana sanya # sannan sai a rubuta abin da ake so ya zamo tag din, misali #BasheerSharfadi shi ne HashTag ɗin da nake amfani da shi a kafafen sada zumunta, don haka idan mutum yayi searching wannan ko ya danna shi a cikin post ɗina, to zai kai shi ya ga duka sauran rubutukan da na yi, ko wani yayi amfani da wannan HashTag ɗin.
Idan wani ya kwafi rubutuna ko yayi sharing to indai da HashTag ɗin a ciki, ina shiga zan gansu gaba ki ɗaya.
Sharuɗan HashTag
- Ba a bada tazara wato Space, idan misali na rubuta #Basheer (space) Sharfadi to iya kalmar Basheer kawai na yi tagging shi yasa ake haɗe shi waje guda domin yin taggin ɗin abu mai ma’ana.
- Ba a saka alamar rubutu, sanya alamar rubutu a HashTag zai bada wahala idan wani yana son ya neme ka, ko kuma wani yayi rubutu game da kai yana so ya sanya, don haka bai kyautu ka saka alamomi irinsu _ ba.
- Sanya kalmomi ko harufan da ba za su wahalar da mutane wajen riƙewa ba, idan ka yi hakan zaka fi samun mutane da yawa, domin wani ko sauraro ya yi zai iya komawa yayi searching domin ganin wannan, hakama idan zai yi rubutu ba zai wahala ba wajen rubutawa.
- Tsayar da abu guda ɗaya wajen HashTag, kaucewa yin hashtag daban-daban misali yau mun yi #SharfadiBasheer gobe kuma mu yi #BasheerSharfadi a’a ka ɗauki guda ɗaya ka yi amfani da shi.
Salon HashTag
Ana yin amfani da salo wanda ba dole bane, wato fara harafin farko da babban baƙi, idan HashTag ɗin ya haɗa sama da kalma ɗaya shi ma haka misali, #WarAgainstFakeNews.
Ire-iren HashTag
- Akwai HashTag na kalmomi ko ƙungiyoyi da hukumomin Gwamnati ko kuma ɗaiɗaikun mutane.
- Akwai HashTag na gari kamar #Kano #Kaduna da sauransu, wanda idan ka yi kana fatana saƙon ya isa ga mazauna wannan gari, shi yasa zaku ga a posting musamman na Instagram da ƴan Kannywood ke yi suna bashi muhimmanci.
Misalan HashTag
#KNSG (Kano State Government), #FactCheking #FakeNews #CITAD#CDDWestAfrica #IDPs #Kano #FreedomRadioNigeria #BBCHausa #Hisbah.
Muhimmancin yin amfani da HashTag
- Isar da saƙon abin da ke ci muku tuwo a ƙwarya ga hukumomi, zaka iya tagging na hukumar da rubutunka ya shafa ta hanyar HashTag, an yi irin wannan lokacin da aka fara batun yaran Kano da aka sace aka sayar a Onitcha.
- Kamfanunuwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da masu sayen kaya na amfani da shi wajen bibiya, misali ina gangami yaƙi da shan ƙwaya, sai nake tagging ɗin kalmomin da suka shafi hakan, to zan ga masu irin wannan gangami a sassan duniya, su ma kuma za su ga nawa, ta nan zaku iya ƙulla alaƙa.
- Gayyato mutane zuwa wajenka, misalin irin wanda ake amfani a Arewa24 za a ce ku biyo mu a HashTag ɗin mu na #Zafafa10 da makamantansu, to ko a Rediyo kake shiri zaku iya ƙirƙira domin wannan.
Da wannan muke bada shawara ga kungiyoyi da marubutanmu kan su samar da HashTag da za su riƙa amfani da shi a rubutukansu.

Inayimaka fatan samun nasara arayuwar ameen.