Da yawa ƴan uwa masu amfani da dandalin sada zumunta na Facebook sun wayi gari da samun saƙo ta Imel mai taken Facebook Protect wanda ke buƙatar mai amfani da dandalin ya amince, sannan ya aiwatar da shi cikin kwanaki goma sha biyar.

A wannan rubutu zamu yi nazari a kan wannan tsari na Facebook Protect da kuma yadda ake shigar sa.

 

Menene Facebook Protect?

Tsarin Facebook Protect da kamfanin Facebook ke neman masu amfani da shi su shiga, shiri ne na sake sanya matakan kariya a asusun masu amfani da shi.

Matakan sanya tsaro a asusun Facebook domin gudun masu kuste, su ne kamfanin ya tattare su waje guda ya basu take da Facebook Protect.

Ka latsa wannan link domin samun ƙarin bayani game da wannan tsari daga kamfanin Facebook.

Kamfanin Facebook yana ɗaukar wannan mataki ne, saboda yawaitar samun ƴan dandatsa da ke yin kutse a asusun masu amfani da shi.

Na san mai karatu shaida ne kan yadda a kullum kuke ganin an yi awon gaba da asusun abokanan hulɗar ku ta Facebook.

Amfani da waɗannan matakan kariya su ne riga kafin da za su bashi kariya daga waɗancan ƴan dandatsa.

 

Duk mai amfani da Facebook ne ya samu saƙon Facebook Protect ta Imel?

Ba kowane mai amfani da shi bane, aka aika wa da wannan saƙo, wanda hakan ke nufin nan gaba za a aika wa wasu.

Wasu kuma dama suna kan tsarin, ma’ana sun riga sun ɗauki matakan kariya a asusunsu don haka a yanzu babu buƙatar sake wa.

Duk da haka zaka iya bincika wa ka gani a asusunka, domin ganin ko ka shiga Facebook Protect ko baka shiga ba.

Me zai faru idan baka shiga tsarin Facebook Protect ba har tsawo kwanaki 15 bayan aike maka da saƙo?

Kamfanin Facebook ya ce, zai hana mutum shiga dandalin matuƙar yayi kwana 15 da samun saƙon Imel amma bai amince da shirin Facebook Protect ba.

 

Yaya ake shiga tsarin Facebook Protect?

Domin shiga tsarin matakan kariyar tsaro na Facebook Protect a asusunka sai ka shiga manhajarka ta Facebook sannan ka bi wannan matakai.

Ka shiga “Settings”

A ciki zaka ga Settings & Privacy

Daga nan sai ka shiga “Password & Security”

A nan ne zaka ga Facebook Protect ko “Check your important security settings.”

A nan zaka shiga inda zaka ga matsayin asusunka game da Facebook Protect, idan ka shiga zai nuna maka “Facebook Protect is On” idan kuma baka shiga tsarin ba zaka ga ya nuna maka “Facebook Protect is Off”, kamar yadda kuke gani a ƙasa.

 

Zaka iya shiga ciki domin amfana da tsarin.

Kana shiga zaka ga ya buɗe maka kamar yadda kake gani a wannan hoton.

Sai ka shiga “Next”.

 

Abubuwan da ake buƙata a Facebook Protect:

Abu na farko da ake buƙata shi ne ka sanya kalmomin sirri wato Password mai tsauri wanda wani ba zai iya kintata ba.

Saboda haka a guji saka suna, ko sunan uwa, uba ko ɗa, maimakon hakan a yi amfani da suna da lamboni da kuma alamomin rubutu, sannan kada ka bai wa kowa password ɗinka.

Abu na biyu shi ne kunna Two-step verification, ƙarin tsaron da zai ƙarfafi password ɗinka, wannan shi zai bada dama ko da ka shiga asusunka da password to ba zai buɗe ba, har sai an aiko maka da wasu lambobi ta lambar waya ko Imel ɗinka domin tabbatar da cewar kai ne.

Saboda haka babu wanda zai iya shiga asusunka sai da wannan, amma ka tabbatar da inganci da tsaron layin wayar da zaka saka a wannan tsari.

Abu na uku shi ne, Login Notification Alert ka kunna ƙararrawa domin sanar da kai a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin shiga asusunka.

Ga ƙarin wasu hotunan yadda zaku gani.

 

Wane amfani tsarin Facebook Protect ke da shi?

Kamar yadda na faɗa a baya, yanzu abu ne mai sauƙi da nan take ƴan dandatsa sun yi awon gaba da asusun Facebook, to wannan tsari abu ne da zai jefa ƴan dandatsa a tsilla-tsilla a duk lokacin da suka yi ƙoƙarin satar asusunka, saboda haka yinsa na da muhimmanci.

4 Replies to “Menene Facebook Protect da ake buƙatar mutane su yi cikin kwanaki 15?”

  1. Mungode

  2. Allah ya saka da alkhairi

  3. Muna godiya da karin haske Allah yakara Basira Karaminsu Babbansu CEO sharfadi. COM

  4. Goga ka san hanya.
    Alllah ya kara basira.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You may use these <abbr title="HyperText Markup Language">HTML</abbr> tags and attributes: <a href="" title=""> <abbr title=""> <acronym title=""> <b> <blockquote cite=""> <cite> <code> <del datetime=""> <em> <i> <q cite=""> <s> <strike> <strong>

*